Daga- Abubakar Sale Yakub
Hukumar Hisbah ta jihar Kano tace ‘tana kyakykyawar fahimtar aiki tsakaninta da ‘yan jaridu, sabanin yadda wasu sukewa al’amarin mummunar fahimta.
Babban Kwamandan Hukumar Sheik Dr. Harun Muhamamd Sani Ibn Sina, ya firta hakan a lokacin da yake zanatawa da wakilin mu Abubakar Sale Yakub ta manhajar WhatsApp daga can kasar Saudiya.
Sheik Harun Ibn Sina, yace “babu wata doka data hana ‘yan jaridu ko masu kawo korafi shiga cikin hukumar Hisbah, Inda yace “akwai dai ka’idoji daya kama kowane mai daukar rahoto ya sani musamman yin hira da wadan da ake zargi da laifi batare da sanin sashin hulda da jama’a ba.
Idan za’a iya tunawa a ranar Larabar data gabata wasu daga cikin manema labarai suka koka na cewar an hanasu shiga cikin hukumar Hisbah daukar labara.
Sai dai zargin da hukumar Hisbar ta musanta tare da cewa “wasune suke ketare iyaka a lokacin da suke gabatar da aikinsu.