Hukumar hisba ta jihar kano da takwararta ta tantance fina finai ta jiha sunyi alkawarin yin aiki tare dan tabbatar da daa tsakanin masu gidajen kallo a fadin jihar kano.
A wani taro da aka gudanar tsakanin hukumar hisba, Hukumar Tace da shugabannin masu gidajen kallo na jihar kano, shugaban hukumar hisba Dr Harun Muhammad Ibn Sina yayi alkawarin hada karfi da karfe dan kauda bata gari tsakanin masu gidajen kallo dake nuna fina finan batsa, inda yaje hankalin hukumomin 3 wajen hada kai da kiyaye dokoki dan cimma nasarar da akasa a gaba na bunkasa tattailin arzikin jihar kano.
A jawabin sa sakataren hukumarTace fina finai ta jihar kano Alhaji Ismaila Naabba Afakalllah bayyana hukumar hisba da cewa hukumace dake aiki dan tabbatar da tsaftace ayyuka badala, wacce zata taka rawa wajen yakin da munanan ayyuka tare da sanya idanu kan gidajen kallo a matsayinta na mai ruwa da tsaki,
Shikuwa shugaban kungiyar masu gidajen kallo na jihar kano Sharu Inuwa Rabiu Ahlan alkawari yayi na bawa hukumomin cikakken hadin kai, inda ya yabawa hukumomin bisa yadda suke tallafawa kungiyar inda yace kungiyarsu bazata bawa gwamnati da alumar kano kunya ba. a makon jiyane gwamnatin jihar kano ta bawa masu gidajen kallo izinin bude gidajen su a wani mataki da gwamnan kano Dr Abdllahi Umar Ganduje yace yunkurine na bunkasa tattalin arziki.