Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga-Abubakar Sale Yakub

Jami’an DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya ta fara shirin daukar matakin ladabtarwa ga jami’anta da aka samu da laifin sakaci da aikinsu a wani hari da akai yunkurin kaiwa shugaba Muhammadu Buubari a jihar Kebbi. 

Jaridar leadership ta rawaito cewa Hukumar bata ji dadin yanda jami’anta suka yi sakaci har wanda ake zargi mai suna Muhammad Jamil ya samu kaiwa ga shugaban kasar ba. 

Da yake tabbatar da bayanin, mai magana da yawun Hukumar, Dr Peter Afunanya ya ce, ” Hukumar ta yi nazarin bidiyon kuma tana nazarin matakin da za ta dauka akan jami’an nata da aka samu da sakaci kan aikinsu.

Ya kara da cewa Hukumar ta DSS na karyata rade-radin da akw yadawa cewa jami’an tsaron shigaban Buhari sun kashe wanda yai kutse ga gungun tsaro inda yai yunkurin afkawa shugaban kasar a garin Argungu dake jihar Kebbi ranar 12 ga watan maris, 2020.

Ya ce” Guddare ya wuce gona da makadi hadi da karya dokar tsaro a kokarinsa na gaisawa da shugaban kasa. 

” jami’an tsaro sun dakatar dashi inda suka bincike shi, inda sakamakon binciken ya nuna bai nufi cutar da shugaban kasa ba, illa kawai shi masoyinsa ne mai wuce gona da iri.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *