
Hukumar HISBAH ta jihar Kano ta tarwatsa taron party na maza da mata da mata yan group din WhatsApp suka shirya a birnin Kano.
Babban Kwamanda Hisbah na Jihar Kano Dr. Harun Muhd Sani Ibn Sina, ya bayar da umarnin jibge Jami’an Hisbah a wani Otal dake birnin Kano, inda matasan suka shirya gudanar da taron sheke agar.
Wannan na kunshene a cikin sanarwar da sashin sadarwa na Hukumar Hisbah ICT, ya fitar .