
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano tace cigaba da baiwa Jami’an horo a kanan Hukumomin Jihar Kano 44, domin su gudanar da aikinsu yadda ya dace.
Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina, ya firta hakan a lokacin daya je rangadin ganin yadda ake baiwa ‘Yan Hisbah horo a kananun Hukumomi 44. wanda aka bude a cibiyoyin Musulunci na Karamar Hukumar birni da Bichi da Karaye da Gaya da kuma karamar Hukumar Rano.
Ya Kuma yi bayani da cewa domin a cimma abin da ake nema hakan yasa tsarin bayar da horon zai zama koyi ka koyar.
Dr. Ibn Sina, ya kuma shawarci ‘Yan Hisbar dasu kaucewa yin dukkan wani abu da ka’iya taba martabar hukumar.
Lawan Ibrahim Fagge
Public Relation Officer.