Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Takardar gargaɗi da hukumar Hisbah ta jihar Kano a arewacin Najeriya ta aika wa wata kafar yaɗa labarai kan batun Black Friday, ranar da kantina ke zabtare farashin kayayyaki, ya ja hankalin ƴan Najeriya.

An ta yawo da wata takarda mai ɗauke da sunan hukumar Hisbah ta jihar Kano a kafofin sadarwa na intanet, mai ɗauke da gargadi ga kafar yaɗa labarai ta Cool FM.

Sunan Black Friday ya samo asali ne shekaru da dama, kuma an daɗe ana bikin Black Friday a ƙasashe da dama inda manyan kantina ke ware ranar Juma’a domin gwanjon kayayyakinsu musamman yayin da shekara ke ƙarewa.

A cikin takardar mai ɗauke da kwanan wata 26 ga watan Nuwamba, hukumar ta bayyana damuwa da kuma koken da ta ce ta samu game da ayyana Juma’a a matsayin Black Friday wato “Baƙar Juma’a.”

“Muna bayyana damuwa kan ayyana Juma’a a matsayin Black Friday, kuma ya kamata a fahimci yawancin al’ummar Kano Musulmi ne da suka ɗauki Juma’a babbar rana.”

“Don haka Hisbah na son a daina kiran Juma’a Black Friday cikin gaggawa,” a cewar takarar ta hukumar Hisbah.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *