
‘Yan bindigar sun hallaka jama’a a kauyukan da ke kananan hukumomin Danmus da Dutsinma da Safana, yayin da mutane da dama suka jikkata a harin na ranar Asabar.
Farmakin ya tilasta wa dimbin jama’a kaurace wa muhallansu.
Kodayake wasu rahotani sun ce, mazauna karkarar sun yi kukan-kura inda suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar, yayin da suka yi ta kona karmami don nuna wa barayin cewa, lallai suna farke.