
Har yanzu ana cigaba da samun mace mace a jihar Kano, adaidai lokacin da gwamnatin Tarayya ta turo tawagar kwararru da zasu bincika lamarin.
Mafi yawancin makabartu dake fadin cikin birnin Kano a kullum sukan cika da masu kai gawa tamkar gidan biki.