Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Ambaliyar ruwa ibtila’i ne da ake yawan fuskanta a yankunan karkara da birane a Najeriya, wadda ke shafar rayuwar dubban mutane.

A duk lokacin da aka samu ruwan sama mai karfn gaske, akan samu asarar rayuka da dukiyoyi ko cunkoson ababen hawa da fargabar rushewar gine-gine.

Mutanen da suka fuskanci wannan ibtila’i tamkar an tilasta musu rasa matsugunnai ne da dukiyoyi da neman wurin mafaka.

Sai dai masana na cewa ana iya kare ambaliyar ruwa idan aka yi tsare-tsare masu inganci musamman a yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya.

BBC ta yi nazari kan yadda za ku iya kare muhallanku daga ambaliyar ruwa, a daidai lokacin da damuna take kara kankama.

A cewar masana wasu matsaloli ne – da a mafi yawan lokaci dan adam ke haifar – ke janyo ambaliya.

A cewar Farfesa Abdullahi Tanko masanin muhalli da ke koyarwa a jami’ar Bayero a Kano, ambaliyar ruwa na faruwa ne duk lokacin da aka samun tsaikon ruwan da ke gudana musamman a lokutan damuna.

Ga dai wasu hanyoyin da ya ce za su iya taimaka wajen kare muhallan ku

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *