Gwamnan jihar Katsina dake arewacin Najeriya Aminu Bello Masari, ya zargi shugabannin rundunonin tsaron kasar da gazawa wajen kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Yayin rabon baiwa mata dubu 1 da kuma dalibai 701 tallafi a karamar hukumar Rimi, Gwamnan jihar ta Katsina ya ce abin mamaki ne da takaici, haka zalika ya gaza fahimtar abinda ya sanya manyan hafsoshin tsaron Najeriya gaza magance matsalar tsaron, duk da cewar dukkaninsu ‘yan arewacin kasar ne, yankin da ‘yan bindigar suka addaba, dan haka kamata yayi a caccaki hafsoshin tsaron amma ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.
Gwamna Masari ya kuma koka kan yadda yace a halin yanzu, ‘yan bindigar na sajewa da mazauna kauyuka a jihar ta Katsina, abinda ke zama karin barazana ga rayukan jama’a.
Ranar 10 ga watan Agustan da muke ciki ‘yan bindiga suka kai farmaki karamar hukumar Kurfi, inda suka sace wata yarinya mai shekaru 13.
A baya dai gwamnan jihar ta Katsina ya yi kokarin cimma sulhu da ‘yan bindigar amma shirin ya gaza dorewa bayan saukin hare-haren da aka samu na takaitaccen lokaci