Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wani jirgin sama a Indiya ya yi hatsari ɗauke da mutum 191 a wani filin jirgi da ke jihar Kerala a kudancin ƙasar.

Jirgin mai suna Air India, ya taso ne daga Dubai wanda yayin sauka ya zame daga titin jirgi inda ya rabe biyu, in ji hukumomi a Indiya.

Rahotanni sun bayyana cewa masu aikin ceto na nan na aiki domin ceto waɗanda ke cikin jirgin.

An dai tabbatar da mutuwar mutum 16, ciki har da direban jirgin.

Wani mai magana da yawun kamfanin jirgin ya bayyana cewa fasinjoji da dama sun samu rauni.

Kamfanin jirgin ya bayyana jirgin na ɗauke da fasinjoji 184 – ciki har da yara 10 da kuma ma’aikatan jirgin bakwai da kuma direbobin jirgin biyu.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na dare a ƙasar, yayin da ake ruwan sama mai ƙarfi.

A watan Mayun 2010, mutum 158 suka mutu bayan jirgin Air India ya yi hatsari a filin jirgin sama na Mangalore a ƙasar.

.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *