Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A baya an shirya cewa shugaban kasar zai bayyana a gaban ‘yan majalisar tarayya domin ya yi masu bayanin abin dake faruwa game da sha’anin tsaro.

Wani fitaccen gwamna daga yankin Kudu ya tasa shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a gaba a kan gayyatar da suka aika wa shugaban kasa.

Wannan gwamna na APC ya nemi jin dalilin da ya sa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya ba ‘yan majalisar dama cewa shugaban kasa ya bayyana a gabansu.

Femi Gbajabiamila ya ce shugaban kasar ya na da damar ya hallara a zauren majalisar ko ya ki.

Jaridar Premium Times da Arise su ka ce a nan aka ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar ya yi fatali da wannan goron gayyata na majalisa.

A gefe guda kuma, gwamnan jihar Yobe wanda shi ne shugaban rikon-kwarya na APC, Mai Mala Buni, ya ce sun cin ma matsaya a game da wannan magana.

Mai Mala Buni ya ce jam’iyya ta yarda cewa shugaban kasa ba zai bayyana gaban ‘yan majalisa ba. Wannan bai yi wa ‘yan majalisar APC da ke taron dadi ba.

Dazu kun ji cewa wani daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC ya yi magana game da wannan batu, ya ce ba shugaban kasa ya kamata ya saurari ‘yan majalisar ba.

Farouq Adamu Aliyu ya bayyana cewa bai kamata Buhari ya amsa gayyatar majalisar da kansa ba, ya ce wannan aikin manyan hafsoshin tsaron kasar ne.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *