Gwamnatin Najeriya ta na shirin cin bashin $1.2 daga wasu bankunan ketare
Wannan bashin kudi da za a ci zai taimaka wajen zamantar da sha’anin noma
Ministan gona ya ce ‘yan kasuwa za su biya wannan bashi nan da shekaru 15
Gwamnatin tarayya ta shiya tsaf domin cin bashin Dala biliyan 1.2 daga wasu bankunan kasar waje da nufin inganta harkar gona a Najeriya.
Punch ta ce za a karbo aron wannan kudi ne daga bankin Dutch Bank da kuma babban bankin nan da ake kira Development Bank na kasar Brazil.
Jaridar ta ce Hadimin Ministan harkar gona, Andrew Kwasari, ya shaida wa ‘yan jarida wannan a Abuja, a ranar Laraba, 17 ga watan Fubrairu, 2021.
Mai ba Ministan gonan shawara yake cewa wannan shiri ya na cikin tsarin Green Imperative Project