
Ma’aikatar ilimi ta tarayyarNajeriya ta bayar da umarnin rufe duk kan manyan makarantu da Makarantun Sakandire da Primary a wani mataki na kau cewa bazuwar cutar coronavirus.
Wanna na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi na kasa Mista Sonny Echono ya fitar.
A cewar sanarwar da aka fitar a ranar Alhmis , Mista Echono, shine ya bayar da umarnin a madadin Ministan iIimi Malam Adamu Adamu,
Ya kuma sanar da cewa duk kan makarantun Hadaka na tarayya (unity schools ) 104 zasu rufe a yau ko Kafin 26 ga watan Maris 2020, a wani mataki na kaucewa yada cutar covid-19 a Najeriya.