Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da sabbin matakai na sassauta dokar kulle da aka kafa a ƙasar domin daƙile yaduwar cutar korona.

Daga cikin sabbin matakan da kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar korona a Najeriya ya sanar sun haɗa da ɗage haramcin tarukan ibadah a Masallatai da coci coci.

Sassaucin na tsawon wata ɗaya ne da zai fara aiki daga ranar Talata biyu ga watan Yuni zuwa 29 ga Yuni. Sai dai shugaban kwamitin na shugaban ƙasa kuma sakataren gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya ce za a sake diba matakan idan wa’adin ya cika.

Sannan an sassauta dokar kulle ta mako huɗu da shugaba Buhari ya saka a Jihar Kano da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona.
Shugaban kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da korona, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja a yau Litinin.

Sai dai Boss Mustapha, wanda shi ne kuma sakataren gwamantin tarayya, bai bayyana takaimaimai abin da sassautawar ke nufi ba a Kano.
Kwamitin na shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar korona a Najeriya ya ce za a buɗe dukkanin kasuwanni, yayin da wa’adin farko na mako biyu na sassauta dokar kulle ke cika a Litinin.

Sai dai Dr. Sani Aliyu, babban jami’i a kwamitin, ya ce za a buɗe su ne na tsawon mako huɗu sannan kuma gwamnoni ne za su tsara yadda za a buɗe su.
Amma dokar hana tafiye tafiye tsakanin jihohi na nan za ta ci gaba da aiki, sai dai dokar ba ta shafi kayayyakin abinci ba da man fetir da sauran muhmman abubuwan bukata.
Sannan gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage dokar haramta zirga-zirgar jiragen sama tsakanin jihohi.
Kwamitin na shugaban ƙasa ya ce an buɗe zirga-zirgar jiragen sama tsakanin jihohi ne saboda sufurin jirgin sama na da tsari.

Dr. Sani Aliyu ya ce su ma jiragen an gindaya musu sharuɗɗan da za su bi kafin su ci gaba da harkoki daga ranar 21 ga watan Yuni.
Sauran matakan sun da haɗa da:
*Jirage za su ci gaba da zirga-zirga a tsakanin jihohi daga 21 ga watan Yuni
Haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi yana nan har sai an sake ji daga gare su
* Dokar hana fita – da ke aiki a Abuja da Legas da Ogun – za ta koma daga 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe
*Makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe
* Otel-otel za su ci gaba da harkoki.
* Tilasta amfani da takunkumi a taron jama’a
Samar da abin wanke hannu da sabulu a wuraren taron jama’a.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *