Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Kano tace zata samar da wata sabuwar doka da zata zama jagorar ma’aurata a fadin jihar nan.
Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya firta haka a lokacin daya kai ziyarar aiki Head Kwatar hukumar Hisbah dake Sharafa.
Yace mutum ya auri matarsa tsahon shekaru daga 30 zuwa 40 amma rana daya sai yace ya saketa’ abin daya kira a matsayin rashin adalci.
Daya juya ga batun mabarata kuwa Gwamnan Ganduje, yace bazata yu wuba ace ‘Yan Jagora surika yawo basa zuwa makaranta duk da cewa ilimi kyautane kuma dole a Jihar Kano.
Da yake jawabi Tun dafari Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano Sheik Dr. Harun Muhd Sani Ibn Sina, ya shedawa Gwamnan Ganduje irin matsalolin da suke fama dash ciki harda rashin motocin aiki da rashin kammala wani gini da ba a karasa ba.

Ganduje, ya sha alwashin kara daukar dakarun Hisbah domin cigaba da kama batagari dake fadin jihar Kano, ya kuma bayar da tabbacin magance duk kan matsalolin da hukumar take fama dasu.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *