Daga-Nura Aliyu

Gwamnatin Kano zata rabawa mata naira dubu 10 domin su dogara da Kansu.
Kwamishiniyar mata ta Kano Dr. Muhammad Umar, ta firta hakan a wajen bikin ranar mata ta duniya wanda ya wakana a dakin taro na coronation a jihar Kano.
Tace mata sun bayar da gagarumar rawa wajen ciyar da kasar nan gaba.
Za’haru Umar, ta shawarci mata dasu nemi ilimin addini Dana zamani su kuma zama masu neman nakansu dan ganin alumma ta gyaru.