Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yace dakarun Hisbah suna aikinsu yadda ya kamata, dan haka Gwamnati zata duba hukumar.
Ganduje, yana mai cewa aikin da Hisbah take a yanzu babu wata gargada ko tangal tangal, kuma a yanzu sai son barka sama da lokacin baya.
Gwamnan yana wadan nan Kalamaine a lokacin ziyarar aikin daya kai Hukumar Hisbah ta jihar Kano dake Shadara a ranar Asabar.
Ya kara da cewa Gwamnatin Kano, zata karasa wasu gine gine dake cikin hukumar wadan da ba’a karasa suba, sannan za’a kara daukar Dakarun Hisbah domin cigaba da kawar da aikin barna a jihar Kano, da kuma yin kira zuwa addinin Allah.
Da yake jawabi Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano Dr. Harun Muhd Sani Ibn Sina, yace suna bukatar Motoci da kayan aiki domin cigaba da kama bata gari.
