Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Sakamakon yadda a kwanakinnan tayi tsami tsakanin gwamnatin jihar kano da da fitaccen malami Abduljabbar Gwamnatin jihar Kanon ta samu izinin kotu domin kulle Masallacin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da kuma hanashi cigaba da wa’azi a fadin jihar.

Gwamnatin ta samu takardar izinin ne daga Alkali Mohammed Jibrin na kotun Majistare dake Gidan Murtala bayan karar da ofishin kwamishanan Shari’ar jihar ta shigar, rahoton Daily Trust.

Kotun ta bada umurnin garkame Masallacin da cibiyar Musulunci dake Filin Mushe, har sai an kammala binciken da hukumar yan sanda da wasu hukumomin tsaro ke yi.

Hakazalika, kotu ta umurci AbdulJabbar ya daina duk wani irin wa’azi da kalaman da ake ganin zai iya haddasa rikici ko rigima.

Hakazalika kotun ta umurci gidajen talabijin, rediyo, da kafafen yada labarai su daina sanya karatunsa har sai an kammala binciken.

Kotun ta umurci dukkan jami’an tsaro su tabbatar da cewa an bi wannan umurni.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *