Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ,ya musanta rahoton kwamitin gwamnatin tarayya da yace ya gano cewa cutar corona ce tayi ajalin kashi 50 zuwa 60 bisa dari na mace mace da suka faru a jihar,

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Abba Anwar ya fitar yace kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ya domin yin bincike kan mace mace ya gano cewa kashi 5.9 cikin dari ne suka mutu a jihar sakamakon cutar corona sabanin wancan rahoton da gwamnatin tarayya ta fitar,

Gwamnan ya ambato kwamitin yana cewa: “Mutum 255 cikin 1604 da suka mutu, wato kashi 15.9… ne suka mutu sanadin cutar korona. Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci saboda fargabar annobar korona.

A makon jiya ne Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a saba gani ba a jihar.

A cewar ministan, an samu rahotonnin mutuwar ne a ƙaramar hukuma takwas na cikin birni a watan Afrilu.

Ya bayyana cewa an riƙa samun mutuwar mutum 43 a kullum lokacin da cutar na kan ƙololuwarta kafin daga bisani adadin ya zama mutum 11 a kowacce rana.

A watan Afrilu Shugaba Muhammadu Buhari ya aika kwamitin na musamman zuwa Kano don gano sanadin yawaitar mace-macen, sannan ya sanya dokar hana fita ko da yake daga bisani Gwamna Ganduje ya kyale mutane su ci gaba da fit

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *