Gwamnatin Zamfara ta ce tana nan tana zuba ido don ganin matakin da rundunar soji za ta dauka kan jami’inta da aka kama
An dai kama jami’in sojan ne yana kai wa yan bindiga makamai da kayayyakin sojoji
Sai dai har zuwa yanzu hedkwatar tsaro bata ce uffam ba a kan batun
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce tana jiran matakin da rundunar soji za ta dauka a kan wani jami’in Soja da aka kama tare da budurwarsa suna bai wa ’yan fashi
bindigogi da kakin sojoji.
Mataimakin shugaban Ma’aikatan gwamnati, Dr. Bashir Muhammad Maru ya ce, Sojoji ne suka kama Jami’in Sojan da budurwar tasa, jaridar Punch ta ruwaito.
Maru ya ce, “Wani batu mai mahimmanci shi ne kame wani jami’in Soja da budurwarsa da ke taimakawa ‘yan fashi da kakin sojoji da alburusai da aka yi kwanan nan tare da sauran masu zagon kasa.
“Yayin da gwamnatin jihar ke jiran matakin da sojoji za su dauka a kan wannan lamarin tare da yin bayani a hukumance, ci gaban ya kara tabbatar da matsayin Gwamna Bello Matawalle na cewa matukar dai ba a tsarkake yakin da ake yi da‘ yan bindiga daga bara-gurbi da masu zagon kasa ba, ba za mu samu nasarar da ake so ba a yakin”.
Lokacin da aka tuntube ta, Hedkwatar Tsaro ta yi alkawarin bayar da sanarwa kan kamun amma ba ta yi hakan ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.