Hakan na zuwa ne sakamakon korafe-korafe da aka shigar na cewa wa’azozinsa na iya haifar da tashin hankali a jihar
Kazalika, gwamnatin ta kuma hana gidajen rediyo da na talabijin saka karatun malamin har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kansa
Majalisar zartaswa na jihar Kano ta dakatar da shahararren malamin addinin musuluncin na jihar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara daga yin wa’azi a fadin jihar baki daya.
Muhammadu Garba, kwamishinan watsa labarai na jihar Kano ya tabbatarwa BBC matakin inda ya ce an tattauna batun yayin zaman majalisar a ranar Laraba sakamakon wasu rahotanni da ke zargin malamin na furta kalamun da ka iya haifar da tashin hankali a jihar.
Ya ce, “gwamnati ta yi nazari kana ta samu rahotanni daban daban har ma daga wasu manyan malamai da hukumomin tsaro, hakan yasa jami’an tsaro kafa kwamiti na musamman don duba kalaman da malamin keyi.”
Ya cigaba da cewa bayan tattaunawa kan lamarin da majalisar zartarwa na Kanon ne aka cimma matsayar cewar kalaman malamin na iya tada zaune tsaye don haka aka bayar da umurnin dakatar da shi daga yin wa’azi a jihar.