Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya soki gwamnatin APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake jagoranta a Najeriya tun 2015.

Jaridar Vanguard ta rahoto gawurataccen ‘dan adawar ya na zargin gwamnatin Muhammadu Buhari da kawo rashin hadin-kai tsakanin al’umma.

Sule Lamido ya nuna hakan ne a lokacin da yake jawabi a ranar Laraba, 20 ga watan Junairu, 2021, wajen rantsar da kwamitin sasancin PDP a Jigawa.

Alhaji Sule Lamido ya ce kafin jam’iyyar APC ta karbi mulki, ta rika zargin gwamnatin PDP da hannu a rikicin Boko Haram da duk wasu zargin sata.

Tsohon gwamnan ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyarsu ta PDP su bada hadin-kai, ya ce kwamitin da aka rantsar zai yi kokarin sulhu ne a reshen jam’iyyar.

A na sa bangare, shugaban PDP na jihar Jigawa, Babandi Ibrahim, yace jam’iyya za ta yi kokarin ganin ta shawo kan wadanda aka yi wa ba daidai ba.

A jiyan ne kuma aka ji Alhaji Sule Lamido, ya na magana game zaben 2023 da ‘dan siyasar nan da ake sa ran zai yi takara a jam’iyyar APC, Bola Tinubu.

Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya rantse cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba mara wa takarar Bola Tinubu baya idan 2023 ta zo ba.

Sule Lamido ya kuma kalubalanci mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya nuna mutanen da yake ikirarin sun fitar da su daga cikin talauci a Jigawa

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *