Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Shehu ya bayyana hakan a shirin Politics Today na ChannelsTV ranar Juma’a inda yace kudi $1billion da aka saki a 2018 don sayen makamai, an yi amfani da su.

Ya bayyana hakan ne yayin tsokaci kan kalaman mai baiwa kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno.

Ma shawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

NSA Monguno ya yi wannan fallasa ne a hirar da yayi da BBC Hausa ranar Juma’a, 12 ga Maris.

Tuni Monguno ya ce anyi masa mumunan fassara ne ba haka yake nufi ba.

Garba yace: “Kana magana kan kudi $1 billion da aka dauka daga cikin asusun rarar man fetur da izinin gwamnoni domin sayen makamai. Ina tabbatar muku cewa ko sisi bai bace ba cikin kudin.”

“Rahotannin da ake yi a hirar da NSA yayi da BBC Hausa, ina ganin an yi masa mumunan fassara.”

“NSA yayi maganganu biyu. Daya shine babu isassun makamai kuma wannan gaskiyane, na biyu shine ba’a gama siyayya ba.”

“Har yanzu ana kan saye; ba abun da za’a saya a kasuwa bane. NSA bai yi zargin almundahana ba, saboda babu wani almundahana cikin wannan lamari.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *