Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon gwamnan Kano kuma jigo a babbar jam’iyar hamayya ta PDP Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga gwamnatin kasar ta janye matakan da ta dauka a baya-bayan nan na kara farashin man fetur da kuma na wutar lantarki, da ya ce za su kara jefa jama’a cikin mawuyacin hali.

Kwankwaso ya ce kamata ya yi gwamnatin ta toshe hanyoyin da kudade ke zurarewa a maimakon karin farashi.

Tsohon gwamnan wanda yanzu haka ke ziyarar karfafa gwiwar magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Edo gabanin zaben gwamnan jihar da za a yi a makon gobe, ya shaida wa BBC cewa babu hujjar karin farashin a wannan lokaci.

Ya ce “Kasashe da yawa a duniya a yanzu shugabanninsu na tausaya musu inda suke fito musu da tsare-tsare ta yadda zasu samu saukin radadin wannan annoba ta korona, amma sai gashi a Najeriya a irin wannan yanayi aka shigo da duka na karin farashin mai da wutar lantarki da dai sauran abubuwa’.

”A gaskiya da wuya ka samu wani wanda zai goyi bayan wannan tsari” in ji shi.

Tsohon gwamnan na Kano ya ce baya goyon bayan wadannan matakai na gwamnati musamman a lokacin da mutane ke fama da matsaloli iri-iri.

“Duk wanda ke wannan kasa ya san da cewa wannan ba lokaci ne na dorawa mutane wannan nauyi ba, don haka ma’anar hakan shi ne sabuwar yunwa da sabuwar matsalar tsaro da sabon rashin aikin yi da dai matsaloli iri-iri da zasu biyo bayan wannan mataki na gwamnatin Najeriya” a cewar Kwankwaso.

Tsohon gwamnan ya ce idan har gwamnatin Buhari na sauraron jama’arta, to yakamata idan tayi abu ba dai-dai ba to ba abun kunya bane ta gyara don a samu ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

” Ita harkar gwamnati akwai maganar kudin shiga akwai kuma maganar kudin da ake kashewa, don haka abin da ake a irin wannan yanayi shine sai a duba aga wadanne kofofi na barna za a toshe, domin akwai hanyoyi da yawa da gwamnati zata iya kawo gyara a kan irin barnar da ake yi”.

Ya ce “Da irin wannan mataki gwamnati ta bi, da ‘yan kasa sun yi murna, sannan sun kuma ji dadi domin kowa abin da yake so shi ne ya samu rayuwa mai kyau”.

Kwankwaso ya ce, bisa la’akari da irin arzikin da Najeriya ke dashi, ba sai anje an dauki wasu matakai da za su dada hargitsa tsarin tattalin arzikin kasar ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *