
Gwamnan jihar Kano , Abdullahi Ganduje, ya nada Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa a matsayin sabon sarkin Rano.
Kafin nadinsa, Alhaji Kabiru dai shi ne hakimin Kibiya kuma Kaigaman Rano.
Ya maye gurbin margayi Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar Ill – Autan Bawo wanda ya rasu a ranar Asabar da ta wuce bayan ya yi fama da gajeruwar jinya.
Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da nadin sabon sakin na Rano a ranar Talata.
Sanarwar da babban jami’in gwamnatin ya fitar ta ce an zabi Alhaji Kabiru Muhammadu Inuwa ne a matsayin sabon sarki, daga cikin hakimai uku da suka hada da hakimin Bunkure da kuma Ciroman Rano.