Daga -Kasim Gambo Kasim
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, shine ya sanar da haka a lokacin da yake kaddamar da daukar malaman Makaranta dubu 7 da dari 6 a filin wasa na Sani Abacha a Jihar Kano.

yace “daga yanzu za’a kama duk kan yaron da aka ganshi yana bara a gidajen mai da guraren haduwar jama’a kuma za’a saka shi a makaranta, tare da kama iyayensa da suka turoshi bara”.