Kawo iyanzu ace tafaru ta kare bayan da gwamnan jihar Edo Godwin Obasake ya sanarda ajiye jamiyyar sa ta Apc, a talatar nan ne ya bayyana ficewa daga jamiyyar bayan dambarwar data barke tsakaninsa da shugaban jamiyyar na Kasa Adams Oshemole abinda yayi sana diyyar soke takararsa duk da cewa shine gwamnan jihar a karkashin tutar jamiyyar Apc da yake neman tazarce karo na biyu,
A jumaar data gabata kwamitin tantance yan takara karkashin jagorancin farfesa Jonathan Ayuba ya mika rahotonsa wanda ya bayyana cire obasake daga jerin yan takara,