Gwamnan jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya ya sake nanata cewa ƙoƙarin murƙushe ƙungiyar Boko Haram na shan zagon ƙasa daga wani rukuni na jami’an tsaron ƙasar.
BBC ta ruwaito Babagana Umara Zulum na cewa ba zai iya yin shiru cikin yanayi na kashe-kashe ba, saboda rantsuwar da ya yi tsakaninsa da Allah a kan zai kare al’ummar jiharsa.
Wannan na zuwa ne yayin da jihar Borno ke ganin ƙaruwar hare-haren ‘yan ta-da-ƙayar-baya, kuma ko a ranar Asabar sai da wani hari ya kashe mutum 15 ciki har da ƙananan yara a yankin kan iyaka cikin ƙasar Kamaru.
Gwamnan dai ya ce akwai buƙatar shugaba Muhammadu Buhari ya san cewa zagon ƙasan da ake yi daga cikin harkar tafi da tsaro na kawo cikas ga ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin ‘yan ta-da-ƙayar-bayan na sama da shekara goma.
Babagana Zulum na jawabi ne gatse-gatse kwanaki ƙalilan bayan kwambar motocinsa mai matuƙar tsaro kwatsam ta yanke tafiya, kuma ya juya ya tsere daga garin Baga na kusa da Tafkin Chadi saboda ɓarin wutar bindigogi babu ƙaƙƙautawa.
Sojoji sun ɗora alhakin abin da ya faru kan Boko Haram. Sai dai Zulum ya nuna cewa da hannunsu cikin abin da ya faru har ya sake amfani da kalmar “zagon ƙasa”.
Wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sada zumuntar gwamnan ta ambato shi yana faɗa wa takwarorinsa gwamnonin APC yayin wata ziyarar jaje ranar Lahadi cewa: “Zan ci gaba da yin tsayuwar daka, daram kan ƙudurin cewa Allah ne kaɗai ke ba da mulki.
Ba na neman wa’adi na biyu, idan ya nufe ni da kammala wannan ma, to na gode Allah. Amma ni a matsayina na gwamna, na yi shiru al’umma jihar Borno miliyan shida su mutu, su ƙare, hakan ba zai zama alheri gare ni ba.
Na yi rantsuwa tsakanina da Allah zan kasance mai gaskiya ga al’ummata,” in ji Gwamna Zulum
Ya kuma tuhumi abin da ya sa sojojin Najeriya suka hana dubban mutanen da rikicin ya raba da gidajensu koma wa gonakinsu a lokacin da su sojoji ke noma a filaye.