Bayan kai ruwa rana da tada jijiyoyin wuya tsakanin shugabannin jamiyyun PDP dake mulkin jihar Edo dana APC dake son dawo da kujerar su da suke ganin anyi musu butulci, a yaune aka fidda sakamakon karshe na kuriun da aka kada a jiya dan sake zaben gwamnan jihar Edo tsakanin Gwamna maici Obaseki da dan takarar Jamiyyar APC Ize Iyamu inda Gwamna Obaseke daya shure takalmin sa yabar jamiyyarsa ta asali APC ya koma PDP sakamakon rikicinsu da tsohon shugaban jammiyyar Adams Oshemole yayi Nasara,
Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa Obaseki ya samu kuria 307,955 inda kuma abokin takararsa Ize Iyamu ya samu 224,619,inda dan takarar SDP ya zama na uku da 323, inda hukumar tace adadin wadanda suka kada kuria 557,443 inda aka samu adadin sahihan kuriun da akajefa 537,407