Gwaman Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sallami mai taimaka masa a bangaren watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu, kamar yadda mai taimakawa gwamnan Kano na musamman kan harkokin watsa labarai, Abubakar Aminu Ibrahim ya sanar a Twitter.
Gwamnan ya ce ya sallami Mr Yakasai ne saboda cigaba da yin maganganu wadanda ba su dace ba da suka sha ban-ban da alkibilar jam’iyyar APC da gwamnatinta da ya ke yi wa aiki.
Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano, Mallam Muhammad Garba, wanda ya fitar da sanarwar gwamnan a ranar Asabar, ya ce an sallamar da aka yi wa Dawisu zai fara aiki nan take.
Ya ce hadimin gwamnan ya gaza banbance tsakanin ra’ayinsa ka kashin kansa da kuma matsayar gwamnati a kan batutuwan da suka shafi jama’a da kasa baki daya.