Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A wata sabuwa daga jihar kano an sake samun mai goyon bayan mika ragamar mulkin najeriya ga yankin kudancin kasar wannan karon gwamna abdullahi Umar Handuje ne ke cewa mikaelwa ga kudancin kasa nada na faidar

Hakan ya biyo bayan goyon bayan da dan majalisar dattijai kuma shugaban kwatin zabe a majalisar Alhaji Kabiru Gaya yayi a kwanakin baya

Wannan karon da ake tunkarar babban zaben da ke tafe a 2023, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kamata a bawa kudancin Nigeria tikitin takarar kujerar shugaban kasa.

Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today a Channels Television da aka haska a ranar Juma’a.

“Kudancin Nigeria ya dace a bawa takara amma ya kamata a samu hadin kai tsakaninsu,” ya ce a yayin da ya ke amsa tambayar game da yankin da ya dace ta fitar da shugaban kasa a 2023.

“Karba-karba duk da cewa bata cikin kundin tsarin mulkin jamhuriyar tarayyar Nigeria tsari ne na cin zabe.”

DUBA WANNAN: Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

Da aka masa tambaya shin ko APC ta tabuka abin a zo a gani tun bayan lashe zabe da ta yi a 2015, ya amsa da cewa eh.

Ya ce jam’iyyar APC a karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ta inganta tsaro sannan tana gyara tattalin arzikin kasar.

Ganduje ya ce yana kyautata zaton jam’iyyar mai mulki za ta yi nasara a babban zaben 2023 da ke tafe ta cigaba da jagorancin kasar.

Amma ya ce akwai bukatar jam’iyyar ta yi shiri mai kyau tare da bincike kan hanyoyin da suka fi dacewa domin sake cin zabe a kasar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *