Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da ranar Litinin 22 ga watan Fabrairu a matsayin ranar komawa makarantu a jihar
Kamar yadda gwamnatin ta amince, gaba daya azuzuwan da basu koma ba suna iya komawa, na makarantun gwamnati da na kudi
Kwamishinan ilimi, Dr Shehu Muhammad ne ya bayyana hakan ranar Juma’a ta wata takarda, inda yace har makarantun islamiyyoyi zasu iya komawa
Gwamnatin jihar Kaduna ra amince da ranar Litinin 22 ga watan Fabrairun 2021 a matsayin bangare na biyu na komawa makarantu a fadin jihar, Daily Trust ta wallafa.
Kamar yadda gwamnatin ta amince, duk azuzuwan SS2, SS1 da kuma JS2 na makarantun gwamnati da na kudi da kuma azuzuwan firamare na 4, 5 da 6 a makarantun gwamnati da kuma azuzuwan firamare 3, 2, 1 da kuma duka azuzuwan Nursery na makarantun kudi da kuma islamiyya duk su bude.