Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe makarantar Leaders International School bayan da ta keta dokar killacewa wadda aka kafa domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Ta kuma soke lasisin makarantar a cewar wata sanarwar da ma’aikatar ilimi a jihar ta fitar.

Makarantar ta keta dokar da aka kakaba a jihar wacce ta umarci dukkanin makarantu su kasance a garkame har sai an tsai da shawara kan lokacin da ya kamata a bude su.

A cewar sanarwar, makarantar ta gudanar da jarabawar shiga ajin JSS1 da SS1 a jiya, 10 ga watan Yuni cikin harabar makarantar.

Bancin rufe makarantar da aka yi, za a kuma hukunta mai makarantar.

Tun ranar 23 ga watan Maris ne dai aka rufe makarantu a jihar Kaduna, kuma ma’aikatar lafiya a jihar ta jadadda muhimmancin mayar da hankali kan karatu ta yanar gizo.

A cikin makon nan ne Gwamnan Nijar Kaduna, Nasir El-Rufai ya dage dokar zama a gida, tare da kuma bude wasu fannoni na kasuwanci da rayuwa a jihar.

Amma duk da haka, gwamnan ya bayyana cewa dole ne makarantu su kasance a rufe, sai masu ruwa da tsaki sun yanke shawara kan lokacin da ya kamata a bude su.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *