Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta aika sako zuwa kaf Nahiyar Turai cikin daren jiya ta hanyar kawar da Real Madrid din data lashe gasar sau 13 daga gasar zakarun Turai.
Gabriel Jesus, wanda ya taimaka gun bude zura kwallon Raheem Sterling kafin ya zira tashi kwallon, ya bayyana cewa City na da yakinin tarihi a yayin wannan gasa.
Lyon zata barje gumi da manchester City a ranar Asabar a wasan kungiyoyi 8, tsakanin su duk wadda ta samu nasara a wasan guda daya a Portugal zataje matakin gaba na kungiyoyi 4.
‘Duk da ana daukar wasan Ya yi mana girma,’ in Jesus, ‘Real babbar kungiya ce, mafi kyawun iya murza leda a wannan gasa. Wannan nasarar tazo ne bayan munyi imani ne mune da nasara. ‘
Sterling ya kara da cewa: ” Ina tsammanin wannan nasarar ta kasance game da yadda mukai kokari ne da kwazo.
“Muna da kwanaki bakwai da za mu shirya yadda zamu fuskanci wasan gaba,” in ji Guardiola. “Ba mu iya doke Lyon a bara ba, gaskiyar magana ke nan. Bari muji daɗi a yau sannan kuma muyi tunani game da Lyon. Zamu tafi Portugal don ƙoƙarin lashe gasar zakarun Turai.
“Manyan kungiyoyi ne suke lashe gasar. Idan mukazo wasan dab da na karshe yayi kyau, fitar da Real yana nufin muna sane cewa zamu iya lashe gasar. Ba mu taba kasancewa a wasan karshe ba ko nasarar lashewa ba, wannan lokacin yanada kyau muyi komai domin ganin nasarar hakan.
“Sauran wasannin duk guda daya ne kuma idan muna tunanin cewa mu karamar kungiya ce. To ai mun doke manyan kungiyoyin – Real, Barcelona, Bayern Munich, Liverpool. Mun doke Real sau biyu. Zinedine Zidane bai taba yin rasshin nasara a wannan a mataki ba. ”
Guardiola ya ga kungiyarsa ta yi amfani da karfi wajen kare martabar ta a cikin wasannin da suka gabata amma yana cike da farin ciki ta hanyar kokarin da yan wasan shi sukayi suka tafiyar da kungiyar da kungiyar zuwa kasar Portugal.
“Zidane yace: Mun rasa wasannin biyu, kuma a karshe kungiyar City ta cancanci hakan,” in ji Zidane. “