Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya shawarci ‘yan siyasan Najeriya da kada su dauki zabe a matsayin juyin mulki ko yaki, a’a su hadu su goyi bayan duk wanda ya samu nasara, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana a Yenegoa, babban birnin jihar Bayelsa yayin bikin nuna godiya / bikin cika shekara daya da Gwamna Douye Diri na mulki, Jonathan ya kuma shawarci wadanda ke cikin siyasa da kada su yi riko da dacin rai.

Tsohon shugaban kasar Naajeriya Goodluck Jonathan ya shawarci ‘yan siyasa da suk daina daukar siyasa da gaba

Goodluck Jonathan ya ce siyasa bai kamata ta kasance kamar juyin mulki ba, demokradiyya ce

Ya kuma ja hankalin masu mulki da su dauki nauyin kowa a inda suke mulki ba iya wadanda suka zabe su ba

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya shawarci ‘yan siyasan Najeriya da kada su dauki zabe a matsayin juyin mulki ko yaki, a’a su hadu su goyi bayan duk wanda ya samu nasara, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana a Yenegoa, babban birnin jihar Bayelsa yayin bikin nuna godiya / bikin cika shekara daya da Gwamna Douye Diri na mulki, Jonathan ya kuma shawarci wadanda ke cikin siyasa da kada su yi riko da dacin rai.

Ya ce, “Tsarinmu na dimokiradiyya doka ta amince da shi, don haka bai kamata ‘yan siyasa na zamani su fara aiwatar da dimokiradiyya da neman mulki kamar muna shirya juyin mulki ba.

“A karshen tsarin siyasa, muna sa ran cewa bangarorin biyu su hadu wuri daya kuma wanda ya ci nasara yana dauke da nauyin kowa.

“Shugabannin da suka fafata a zabe dole ne su san cewa tsari ne na siyasa wanda doka ta sani, kuma duk wanda ya yi nasara, mun yarda cewa Allah ne Ya ba shi wannan matsayin.

“Ina son na gode wa Gwamna Diri saboda bude hannuwansa da kuma maraba da duk wani dan jihar Bayelsa, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba. A lokacin da ka ci zabe a lokacin ka zama gwamnan kowa,” in ji shi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *