
An samu wata girgizar kasa mai karfin degree 2.7 a ma’aunin Ritcher wadda ta auku a yankin Qunfudah dake yankin garin Makkah.
Rahoton kamfanin dillancin labarun kasar Saudiyya, SPA ya tabbatar da haka, inda ya ce lamarin ya auku ne a daren Juma’a, gabanin Musulmai su dauki haramar azumin Ramadan.
Sai dai da yake girgizar kasar bata yi karfi ba, amma wasu mazauna garin sun ji karbar , kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Kakaakin hukumar Saudi Geological Survey, SGS, Tariq Ab Al-Khalil ya tabbatar da aukuwar girgizar kasar, amma yace ba wannan bane karo na farko da ake samun hakan ba.
“Koda yake ana daukan tsawon lokaci kafin samun irin haka, amma ana yawan samun motse motse a cikin kasa a yankin, irin wannan girgizan ba shi da tasiri saboda ba shi da karfi, jama’a kadan ne suke iya fahimtarsa.
“Hukumar SGS na kula tare da sa ido a duk wani girgizar kasar da aka samu a masarautar Saudiyya gaba daya, don haka jama’a su kwantar da hankulansu, kada su firgita.” Inji shi.
Daga karshe Tariq ya yi addu’ar Allah Ya kare kasar Saudiyya daga dukkan sharri.
A hannu guda gwamnatin kasar Saudiyya ta amince a gudanar da Sallar asham a Masallacin Makkah duk da umarnin da ta baiwa jama’a da su yi sallolinsu a cikin gidajensu.
Sai dai an gudanar da sallar ne ba tare da wasu jama’a da yawa ba, daga limami sai wasu yan mutane kalilan da suka hada sahu da bai wuce biyu ba.