Ana ci gaba da jimamin mutuwar iyalan gida guda da gini ya ruftawa a ƙaramar hukumar Arewa da ke jihar Kebbi.
Lamarin ya faru ne a daren Litinin inda ginin ya faɗa wa iyalan gidan Malam Ɗantani yayin da suke bacci, sai dai babban ɗansu ya tsira kasancewar ba ya ɗakin lokacin faruwar lamarin.
Ɗan majalisar dokokin jihar ta Kebbi mai wakiltar ƙaramar hukumar ta Arewa, ya ce ginin ya rusowa mutanen ne sakamakon mamakon ruwan sama da ake zabgawa a yankin.
Ya ce ginin da suke ciki na laka ne, kuma ya yi rauni ne saboda yawan ruwan saman da ake fuskanta. Tuni dai aka yi jana’izar iyalen a ranar Litinin.
Sai dai babban ɗan ma’auratan ya tsira kasancewar ba ya ɗakin lokacin faruwar lamarin a ƙauyen Tungar Gyado.
Garba Muhammad Yeldu ne shugaban karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi, ya kuma yi wa BBC ƙarin bayani kan lamarin.
“Kafin su rasun ma har matar gidan ta shiga maƙwabta da su ma gininsu ya faɗi ta yi musu jaje, to komwarta gida kenan ita ma nasu tsautsayin ya same su.