Gasar cin kofin Dan Isan Katsina ta sauya fasalin kwallo kafa a karamar hukumar Kankiya,
Wasan kwallon kafa na kan gaba wajen daukar hankalin matasa a duniya inda zakaga koina yara da matasa na kafa raga karama ko babba, ta karfe ko katako, itace ko Kara kai wani lokaci har bishiyu da suke tsaye kan iya zama ragar wasan kwallon kafa,
Jihar katsina na daya daga cikin jihohin Najeriya da matasanta sukayi shura wajen son wasan kwallo tun jihar na hade da jihar kaduna inda wasan kwallon kafa yayi tashe a shekarun baya, ba ada birnin jihar ta katsina kananan hukumomin jihar suma baa barsu a baya ba inda a kullum yara masu tasowa da samari ke tururuwar zuwa filin kwallo dan motsa jiki,
Karamar hukumar kankiya na daga cikin kananan hkuumomi da matasan garuruwan da sukayi karamar hukumar ke da burin ganin wasan ya bunkasa dan samar da yan wasan da zaayi alfahari dasu tare da hada kan matasan guri guda dan bunkasa cigaban yankin,
Garin Rimaye dayane daga cikin garuruwan da ake hada wasanni dake daukar hankalin kananan hukumomin,Malunfashi, Funtuwa,Batsari da suran kananan hukumomi dake makaftaka da inda ake buga wannan wasa,
Gasar cin kofin Dan Isan Katsina wacce Ministan sufurin jiragen Sama Hadi Sirika ya sanya da ake gudanarwa a garin Rimaye ta zama abar kwatance da koyi tsakanin garuruwa da kananan hukumomin jihar duba da yadda ake gudanar da gasar da tsarin da gasar ke dashi,
Wani abin shaawa shine yadda mutane ke fita kallon wasan a duk lokacin da akeyi da yadda manya da Matasa ke bin wasan ya sanya makwafatan yankin yi tururuwa dan ganin kowane wasa, duk da cewa tsarin gasar na wasan hadaka ne wato GALA inda ake fara wasan tun safe har yamma hakan bai hana mutane zama dan kashe kwarkwatar idanunsu ba tun fara gasar har kawo yanzu da aka shiga wasan daf dana kusa dan karshe ciki harda wasan da ake yiwa taken “Final before the final” wato wani wasan hammaya tsakanin Rimaye da …….inda wasan yakai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Coach Ashiru Abubakar Sukuntuni dayane daga cikin Masu kungiyoyi dake fafatawa agasar a tattaunawarsa da wakilin mu ya bayyana irin gudunmawar da Minista Hadi Sirika ya bayar dan ganin any gasar ta bana,
Daga cikin kungiyoyin da suke buga gasar sun hadar da,Valencia, fc Porto,Italy Rimaye,Arewa Kankiya,Rimaye United,Golden Star,Yar Gwanda,Super Star da sauransu,
Gasar ace ta zama zakaran gwajin dafi tsakanin takwarorinta a jihar katsina kawo iyanzu duba da kulawar data samu daga Minista Hadi Sirika a kokarinsa na hada kan alummar jihar katsina,birni da kauye ta hanyar wasan kwallon kafa, wasan da akayi Itifaki shine abu daya tilo dake hada kan alumma a lokaci guda.