
Gwamna Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR ya bada sanarwar janye dokar hana zirga zirga na kwana biyu daga Litinin zuwa Alhamis mai zuwa wato 4 da 5 ga watan Mayu daga karfe 10am na safe zuwa karfe 4pm na yamma domin bawa al’ummar jihar Kano dama su fita neman kayan abinci musamman a wannan watan Ramadan mai alfarma.
Gwamnan ya yi kira ga alummar Kano dasu bi ka’idojin da aka shimfida na rage cunkoso da cudanya da mutane kuma a saka takunkumi a fuska wato face mask sannan a dinga tsaftace hannu domin hana yaduwar cutar Corona wato Covid-19.
Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
May 2, 2020.