
A kokarinsu na tallafawa alummar jihar Kano ‘Yan asalin kasar Lebanon ma zauna, Jihar nan, suka bayar da tallafin kayan abinci da sauran kayayyaki da suka shafi lafiya na sama da naira miliyan 100, dan rabawa marassa karfi.
Da yake gabatar da kayayyakin ga Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Karamin Jakadan Lebanon dake Kano, Khaleel Musulmaniya,
yace kayan sun hadar da shinkafa tan 30 da katan katan na Taliya dubu biyu.
Da yake mai da jawabi Gwamna Gaduje, ya godewa ‘yan kasar Lebanon , inda yace suna zaune a jihar Kano sama da shekaru 100, sannan duk abin da ake dan cigaban kano dasu ake yi, dan wasun su kakanninsu da iyayensu duk a nan Kano aka haife su.
Bayan karbar kayayyakin nan take Gwamnan Ganduje ya mikasu ga shugaba kwamitin asusun tattara kayan taimakon covid-19, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, wanda ya jinjinawa Yan Lebanon, tare da bayyanasu a matsayin wadan da sukeyin bakin kokarin su dan cigaban Jihar Kano.