Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke fadin Jihar.

Gwamnatin jihar Kano ba ta bayyana dalilin rufe makarantun ba a cikin gajeriyar sanarwar da kwamishinan ilimi, Sanusi Kiru, ya fitar, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

“Mai girma gwamna ya bayar da umarnin gaggauta rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu ba tare da bata lokaci ba.

Legit.ng ta wallafa labarin cewa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana manyan dalilan da suka sa shi ya tuɓe Muhammadu Sunusi II daga karagar sarkin Kano, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Gwamnan ya bayyana tuɓe sarkin a matsayin matakin gaggawa don ceto tsarin mulkin masarautar gargajiya daga kama-karya.

Gwamna Ganduje ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin ƙaddamar da wani littafi da aka rubuta akan rayuwar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, wanda shahararren dan jaridar nan, Bonaventure Philips Melah, ya rubuta kuma ya wallafa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *