Daga- Salisu M.Jegus

Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood Adam A. Zango ya ce ya yi rijista da hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano ne domin kawo karshen matsalolin da abokan sana’arsa suke fada wa a cikin na rashin amincewa da fina-finansu.
Jarumin ya shaida wa kafar BBC cewa yin rijistar tasa zai ba shi damar zuwa Kano domin gudanar da sana’arsa ba tare da shamaki ba.
Inda yace, “Na dawo na yi rijista da censorship board ne saboda dalilai biyu: na farko shi ne, furodusas dina da suke yin fina-finai da ni a jihar Kano a nan suka fi yawa.
”Sannan kuma yarana da nake tare da su da wadanda nake mu’amala da su dukka suna samun matsaloli wajen ba a kiran su ayyuka a dalilin rashin rijistar da ban yi ba. Wadansu ma sun yi rijista amma ba sa samun aiki saboda suna tare da ni.”
Zango ya kara da cewa bai kamata son zuciya ya sanya shi ya zama silar hana wasu da ke kusa da shi samun aiki ba.
Sai dai ya kara da cewa har yanzu bai koma kungiyar Kannywood ba, yana mai cewa “ina nan a matsayin dan wasan fina-finai mai zaman kansa da ke Kaduna.”
A watan Fabrairu ne hukumar tace fina-finai ta ce dole jarumin ya bi dokokinta idan yana so ya je jihar domin gudanar da harkokin fim.
A wancan lokacin Adam A. Zango ya fito a wani bidiyo da tauraruwa Rahama Sadau ta wallafa a Instagram yana yi wa masoyansa Kanawa albishirin cewa zai je jihar domin kallon fim din ‘Mati A Zazzau’.
Sai dai jim kadan bayan hakan ne wasu kafafen sadarwa na zamani suka ambato shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar, Isma’ila Na’abba Afakallah, yana shan alwashin kama tauraron idan ya sanya kafarsa a jihar.
Amma a tattaunawarsa da BBC, Afakallah ya ce ba su hana tauraron shiga jihar ba amma suna da dokoki game da zuwansa.
“Idan zuwa zai yi ya kalli fim kawai ya tafi shikenan, akwai wadanda ba su da rajista kuma suke zuwa su yi kallon su tafi babu ruwanmu da su.
“Kwanakin baya wannan hukumar ta yi kokarin tantancewa da tsafetace masu ruwa da tsaki a wannan harka kamar yadda doka ta ba ta dama.”