Daya daga cikin fitattun mawakar hausa a arewacin najeriya Alhaji Hassan Wayam Ya rasu,
Wayam wanda yayi fice a kidan kukuma ya shahara kwarai wajen yiwa fitattatun mutane waka musamman matasa dake tashe a fannoni daban daban na rayuwa wakokin Marigayi Hassan Wayam cike suke da Ilimi da waazi a wasu lokutan hadda barkwanci da zambo,
Ma biyan Wakokin Hassan wayam sun tabbatar da cewa yana daya daga cikin yan gayun mawaka a wancan lokaci da matasa ke koyi da irin Adonsa musanman shigarsa ta manyan kaya da falmaran daku karkata Hula zanna bukar akan Cikon Daya tara
Haifaffen garin Gwadda a Karamar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara ya kware wajen yiwa sojoji waka a tun shekara ta 1969 inda sojojin ke sonsa kwarai ya rasu a Zaria in yakoma da zama bayan ya bar garin Mayanci yabar mata, ya’ya da Jikoki da dama.