,
Hukumar wasan kwallon kafa ta duniya fifa ta dakatar da shugaban hukumar kwallon kafar afirika Ahmad Ahmad shekara 5 saboda laifin almundahana da kudaden hukumar,
Bayanin dakatarwar ya fito a lokacin da shugaban dan kasar Madagascar ke gangamin sake zabensa, tare da cin tararsa kudi Dollar Amurka 220,000,
Shugabancin Ahmad na shekaru hudu cike yakeda kalubale da zarge zargen kashe kudade ba bisa kaida ba da rashin iya gudanar da shugabanci a hukumar,
Ko a baya bayan nan kwamitin Da’a na hukumar ya sami Ahmad Ahmad da laifin yin amfani da kudaden hukumar wajen biyar Umrah ga wasa shugabannin hukumomin kwallon kafa na wasa kasashe.
A ranar 12 ga watan maris ne za a gudanar da zaben shugabanicin hukumar a rabat ta kasar morocco, a shekara ta 2017 ne aka zabe Ahmad Ahmad a matsayin shugaban hukumar kwallon kafar Afirika baysn samun samun goyon bayan humumar kwallon kafa ta duniya.