Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Saye da sayarda da miyagun kwayoyi shine sular cigaban lalacewa da dagulewar cigaban rayuwar matasa.

EXPRESSRADIOFM.COM ta tautauna da Tsohon dan majalisar Tarayya na karamar hukumar Birnin Kano (Kano Municipal) Dr Abubakar Nuhu Danburam, inda ya yi kira da matasa da suyiwa Allah su guji shan miyagun kwayoyi domin samun cigaban rayuwar su da samun zaman takewa cigaban al’umma kamar kowa.

Dr Danburam yace” tunkawo da cigaban rayuwa jigonsa matasa ne, mafiya yawan al’umma a duniya matasa ne, idan rayuwar matasa ta lalace dukkan al’amuran rayuwa zasu gurbace, duk matashin da ke shan kayan maye tabbas rayuwarsa gurguwa ce kuma mutane zasu kyamace shi.

Abu na farko da yakamata dukkan wani mai neman tsayawa takara yakamata yafara jan hankalin al’umma shine hana saida miyagun kwayoyi da kuma hana shansu, duk sanda shugaba yai kokari ya hana koda matashi guda dayane shan kayan maye tabbas ya yi babban jahadi.

Yakara da cewa “mafiya yawa masu ta ammali da kayan maye matasa ne, kuma matasa sune mafiya saurin kawo sauyin rayuwa da zaman takewa mai kyau ko maras kyau a al’umma, don haka rayuwar matasa abar dubawa ce da ba ta kulawa mai karfi.

Duk sanda aka rasa tunani mai kyau ko tarbiyya a tare da matasa to rayuwar kowa tana cikin matsala, domin matasa sune jigon rayuwa.

Ina kira da gomnati da tafi baiwa bangaren hana sha da sayarda miyagun kwayoyin-maye fifiko fiye da sauran bangarori na jindadin rayuwa, domin sai rayuwar matasa tayi kyau sannan ne komai zai zama abin moriya cikin jindadi.

Idan gomnati na watsar da lamuran matasa ba tare da basu kulawa ba, tabbas rayuwa zatai muni ga kowa.

Dr Danburam yace ” idan unguwar da kuke akwai matasa ku taimaka musu kununa musu kauna da kulawa, domin duk matashin da ka taimakawa, kuma ka nunawa kulawa ba shakkah duk abinda kafada masa yabari ko yadaina zaiji maganar ka kuma zai daina, dukkan kuwa matashin da ka rabu dashi sai yazo ya yi abinda ba daidai sannnan zakai masa fada ko ka hanashi to ba shakka bazai dauki abinda kafa masa ba, saboda yasan baka damu da rayuwarsa ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *