Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya ce ya gana da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ne domin tattaunawa kan “halin da kasa ke ciki da harkokin siyasa da matakan da za a dauka don cigaba.”

Fani-Kayode, a jiya ya gana da Shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

Hotunan taron na su ya sanya wasu sun fara hasashen cewa Fani-Kayode wanda dan jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne na shirin sauya sheka ne zuwa APC duk da cewa yana cikin manyan masu sukar jam’iyyar.

A sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Twitter a ranar Talata, Fani-Kayode ya ce taron da suka yi na sada zumunci ne da hada hannu domin ceto Nigeria daga tsindumawa cikin yakin basasa.

Ya ce baya ga shugabannin na jam’iyyar APC, yana ganawa da shugabannin wasu jam’iyyun siyasar.

“A jiya, na gana da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Buni na Yobe da Gwamna Yahaya Bello na Kogi. Mun tattauna halin da kasa ke ciki, siyasar jam’iyyu da yadda za a ciyar da kasa gaba,” a cewar wani sashi na sanarwarsa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *