
Damuwar da fadar shugaban Najeriya ta nuna game da yadda wasu gwamnonin jihohin suke yin gaban kansu a yaki da cutar korona ta jefa alamar tambaya kan yadda ake yaki da cutar.
A tattaunawarsa da BBC, Malam Garba Shehu, mai taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin watsa labarai ya ce abin takaici ne a ce gwamnatin tarayya tana daukar matakan yaki da annoba amma ana samun matsalar hadin-kai daga gwamnonin jihohi.
Ya ce ”ba wai zargi muke yi ba ko kushe, amma akwai bukatar a ce ana tafiya tare saboda idan matsaya ba ta zo guda ba, da wuya a yi nasara a yaki da korona”.
Malam Garba Shehu, ya ce kwamitin da ke yaki da annobar na kasa na kokawa kan yadda matakan wasu jihohi ke warware nasarorin da ake samu akan annobar.
“Kamata ya yi kafin a dauki kowanne irin mataki, to a tuntubi masana domin neman shawarwari,” in ji mai magana da yawun shugaba kasar.
Ko da yake kakakin na Buhari bai fito karara ya ambaci sunan wani gwamna ba, amma masana harkokin yau da kullum suna ganin yana shagube ne a kan matakan da wasu gwamnoni irin su Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Gwamna Aminu Bello Masari da Gwamna Dapo Abiodun da Gwamna Nasir El-Rufai da ma wasunsu da dama kowanne yake yin gaban kansa a yaki da cutar ta korona.