Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Fadar shugaban Najeriya ta yi karin haske kan abin da take ganin ya jawo yanayin tsadar rayuwa da tashin farashi da ‘yan kasar ke ta korafi a kai.

A wata hirarsa da BBC Hausa, mai bai wa shugaban kasar shawara kan harokin yada labarai Malam Garba Shehu ya ce abu uku ne suka jawo halin tsadar kayayyaki da ake fuskanta amma batun rufe iyakokin kasar ba ya daga cikinsu.

A ranar Laraba ne ‘yan Najeriya da dama suka taso Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a gaba, inda suke ta sukarsa sakamakon tsadar rayuwa a ƙasar.

Ƙarin da aka yi na farashin wutar lantarki da man fetur na daga cikin abubuwan da suka harzuka wasu ‘yan ƙasar suke sukar shugaban inda har wasu ‘yan arewacin ƙasar ke ƙalubalantar shugaban kan cewa ya nuna musu aikin da ya yi musu a tsawon mulkinsa.

Sai dai a ranar Alhamis, shugaban ya bayyana damuwa kan tsadar kayayyakin abinci da ƴan kasar ke kokawa da gwamnatinsa.

Har ma Shugaba Buharin ya ce gwamnatinsa ta damu kan tsadar kayayyakin a daidai lokacin da kullen korona ya ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin wani hali, a wata sanarwa Malam Garba ya fitar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *