Hukumar yan sandan farin kaya, SSS, ta musanta zargin da ake yi na cewa ta kama Salihu Tanko-Yakasai da aka fi sani da Dawisu
Wannan zargin na cewa ne bayan batarsa tun ranar Juma’a da ake dangatawa da wani sako da ya wallafa a Twitter na sukar Shugaba Buhari da APC kan tsaro
A bangarenta, hukumar ta SSS reshen jihar Kano ta ce Salihu abokinta ne, ba ta kama shi ba kuma bata gayyaci shi ba
Hukumar yan sandan farin kaya, SSS, reshen jihar Kano, ta musanta kama Salihu Tanko-Yakai, hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje saboda kalaman da ya yi na sukar Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC mai mulki, Daily Nigerian ta ruwaito.
Idan za a iya tunawa a yayin da aka sace yaran yan makaranta a jihar Zamfara, Mr Tanko Yakasai wanda ake fi sani da Dawisu, ya shafinsa na Twitter ya bayyana cewa gwamnatin APC ta gaza.
Jim kadan bayan wallafa sakon, an rasa gano inda Yakasai ya ke a cewar abokansa don haka aka fara zargin cewa jami’an yan sandan farar hula na SSS ne suka yi awon gaba da shi.
Mr Alhassan ya ce: “Ba mu kama Salihu ba, ko gayyatarsa ma ba mu yi ba, kada mu kanta shi abokin mu ne, ya kan bamu shawarwari kan muhimman batutuwa da suka shafi tsaro a Kano.”